Maganin

Maganin Basir Kowanne Iri da Alamomin sa

Da farko dai a cikin duburar ‘dan Adam akwai jijiyoyin jini wadanda wani lokacin suna samun matsatsi da talala mai takurasu. A lokacinda suka samu takurawa da yawa, sai su kumbura.

Kumburin wadannan jijiyoyin jini da kara matsi da takura a garesu cikin dubura shi ya ke sa wa kaga wani tsiro ya fito maka a bakin dubura, wanda jijiyar jini ce.

Za ka ji ciwo, ko kai-kayi koma zubar jini.

Wannan shi ake cewa BASIR-MAI-TSIRO. Da akwai kuma nau’in Basur mai sanya yawan fitar hutu wato tusa da kuma mai sa cushewar ciki ko yin kashi mai tauri. Wani basir din kuma har yana sa tsatstsagewar dubura yayin fitar bayan gida.

Alamomin da Mutum Zai Gane Yana Dauke da Basur

Mutum zai rika fama da wadannan matsaloli

  • Kaikayi a dubura da bacin rai.
  • Fitar jini idan ana bayan gida amma ba tare da anji zafi ba.
  • Ciwon jiki da rashin sakewa.
  • Kumburar dubura.
  • Fitar kashi curi-curi ko dunkule-dunkule tare da wahala.

Maganin Basur Kowanne Iri

A samu

  • sassaqen itacen mangwaro,
  • sassaqen kadanya,
  • sassaqen dorawa,
  • da sassaqen madaci amma madacin kadan ake bukata.

Sai a hade su wajedaya a wanke a zuba jar kanwa kadan.

A tafasa, kullum a sha rabin kofi sau uku kafin a ci abinci.

Idan kuma basur din mai tsiro ne ko wanda ake fitar baya, to idan an tashi sai a tafasa magungunan a zuba ruwan a cikin babban mazubi. Sai ka tsuguna, tururin ya dinga shiga karkashinka, idan ya dan huce kuma sai a shiga ciki a zauna tsawon yan mintuna ko kuma a dinga kama ruwa da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button