Maganin

Maganin Tusar Gaban Mace (Budurwa ko Matar Aure)

Wannan matsala tana haddasa fitar iska daga gabar mace kamar tusa (fut! fut!). Yana iya zama abin kunya, musamman a lokacin kwanciyar aure. Ga wasu dalilan da ke haddasa hakan:

Dalilan da ke kawo tusar gaba:

  • Zama a kasa a kan tiles (musamman idan akwai AC) ba tare da wando ba.
  • Yawo a gida ba takalmi ko slippers, musamman a sanyi ko tiles masu sanyi.
  • Kwanciya ba wando a karkashin fan (fanka) yana sanyaya gabanki sosai.
  • Rashin yin tsarki da ruwan zafi bayan al’ada ko jima’i.
  • Barin maniyyi ya kwana a ciki ba tare da yin wanka ko tsarki ba.
  • Yawan amfani da kayan mata ba tare da dalili ko izini daga masani ba.
  • Cushe-cushen kayan matsi da dama cikin farji ba tare da sanin abun cikin su ba.
  • Matsanancin ciwon sanyi (infection) wanda ke cinye lafiyar farji da mahaifa.
  • Rashin iya ‘position’ a lokacin kwanciyar aure, wanda ke iya kawo rauni.
  • Zama da pant guda daya daga safe har dare, yana sa gaban mace yayi danshi da warin kamshi.
  • Rashin daure zani da kyau ga matan da suka haihu, yana barin farji a bude.
  • Cikin yunwa ko rashin cin abinci musamman a lokacin al’ada ko Jego.

Hanyar Magance Tusar Gaban

Magani na 1: Dafa da shan turaren ganyayyaki

Abubuwan da ake bukata:

  • Ganyen Magarya
  • Gabaruwa
  • ’Ya’yan Hulba
  • Gishiri

Yadda ake hadawa

  • Ki dafa waɗannan kayan a tukunya.
  • Ki zuba gishiri kaɗan a ciki.
  • Bayan sun dahu sosai, sai ki dinga shiga ciki kina “seat bath” na tsawon minti 20.
  • Bayan kin fito, zaki ga wani bakin abu yana fita daga gabanki — wannan alama ce ta tsaftacewa.
  • Bayan haka, ki nemi farin muski, ki dangwala da auduga mai tsafta, ki dan matsa gabanki da shi.
  • Ki nemi angurya da ’ya’yan auduga ki dinga turara gabanki da su don ƙarin tsafta da kamshi.

Shawara

  • Karki yi amfani da duk wani kayan mata ko matsi ba tare da shawarar kwararre ba.
  • A rinka canza pant sau da yawa, kuma a dinga amfani da auduga
  • Gyaran jiki ga mata zallah

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button