Maganin
Maganin Tusar Gaban Mace (Budurwa ko Matar Aure)
Wannan matsala tana haddasa fitar iska daga gabar mace kamar tusa (fut! fut!). Yana iya zama abin kunya, musamman a lokacin kwanciyar aure. Ga wasu dalilan da ke haddasa hakan:
Dalilan da ke kawo tusar gaba:
- Zama a kasa a kan tiles (musamman idan akwai AC) ba tare da wando ba.
- Yawo a gida ba takalmi ko slippers, musamman a sanyi ko tiles masu sanyi.
- Kwanciya ba wando a karkashin fan (fanka) yana sanyaya gabanki sosai.
- Rashin yin tsarki da ruwan zafi bayan al’ada ko jima’i.
- Barin maniyyi ya kwana a ciki ba tare da yin wanka ko tsarki ba.
- Yawan amfani da kayan mata ba tare da dalili ko izini daga masani ba.
- Cushe-cushen kayan matsi da dama cikin farji ba tare da sanin abun cikin su ba.
- Matsanancin ciwon sanyi (infection) wanda ke cinye lafiyar farji da mahaifa.
- Rashin iya ‘position’ a lokacin kwanciyar aure, wanda ke iya kawo rauni.
- Zama da pant guda daya daga safe har dare, yana sa gaban mace yayi danshi da warin kamshi.
- Rashin daure zani da kyau ga matan da suka haihu, yana barin farji a bude.
- Cikin yunwa ko rashin cin abinci musamman a lokacin al’ada ko Jego.
Hanyar Magance Tusar Gaban
Magani na 1: Dafa da shan turaren ganyayyaki
Abubuwan da ake bukata:
- Ganyen Magarya
- Gabaruwa
- ’Ya’yan Hulba
- Gishiri
Yadda ake hadawa
- Ki dafa waɗannan kayan a tukunya.
- Ki zuba gishiri kaɗan a ciki.
- Bayan sun dahu sosai, sai ki dinga shiga ciki kina “seat bath” na tsawon minti 20.
- Bayan kin fito, zaki ga wani bakin abu yana fita daga gabanki — wannan alama ce ta tsaftacewa.
- Bayan haka, ki nemi farin muski, ki dangwala da auduga mai tsafta, ki dan matsa gabanki da shi.
- Ki nemi angurya da ’ya’yan auduga ki dinga turara gabanki da su don ƙarin tsafta da kamshi.
Shawara
- Karki yi amfani da duk wani kayan mata ko matsi ba tare da shawarar kwararre ba.
- A rinka canza pant sau da yawa, kuma a dinga amfani da auduga
- Gyaran jiki ga mata zallah