Maganin

Maganin Ƙarin Ƙiba

wanan magani zai taimaka wajen karin kiba

Abubwan Daza’a Naimu

  • Man Hulba
  • Zuma
  • Sassaƙen kuka
  • Chukwi
  • Aya
  • Ɓawon Kankana

Yanda Za’a Hada Maganin Ƙarin Ƙiba

  • Asamu Man Hulba sai a gaurayashi da zuma mai kyau adinga shan chokali biyu mintuna 30 kafin aci abinci. Safe da rana da dare. Za’asha na tsawon sati 3.
  • Asamu Sassaƙen babbar bishiyar kuka adaka ashanya yabushe asake dakawa yazama gari sai asamu Aya asoyata sama-sama adaka tazama gari, sai asamu Ɓawon Kankana abusar dashi adaka yazama gari, sai asamu Chukwi adaka yazama gari.

Waɗannan garin sai ahaɗasu guri ɗaya (awunsu yazama daidai) sai a kwaɓa da zuma adinga shan chokali 2 bayan anci abinci. Safe da rana da dare.

Sannan za’a iya gauraya wannan haɗin garin da ruwan Kankana asa madara adinga sha.

Za’asha na tsawon sati uku

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button