Maganin
Maganin Ciwon Hakori
Yau kamar yadda yan uwa suka bukaci a kawo musu maganin ciwon hakuri, to yau Allah ya nufa gashi mun kawo.
Kuma wannan fa’ida tana da karfi da tasiri sosai da sosai, abin bukata kawai a samu ingredients din ya zama original.
Abinda zaa naimu
- Man kanin fari(clove oil)
- Garin kaninfari (clove powder)
Yadda Zaa Hada Maganin Ciwon Hakori
- Idan hakurin ciwo yake ko rawa ko radadi,to sai a samu man kaninfari a dankwalo da auduga a lika a wajen zuwa minti sha biyar sa a cire,ai haka sau biyu a rana.
- Idan kuma yayi rami to sai a samu garin kaninfari kadan a kwaba shi da man kaninfarin,sai a dauki kadan a dika a wajen lokacin kwanciya bacci,zuwa safiya a kuskure baki a zubar.
Insha Allah duk mai fama da ciwon hakuri yayi amfani da wannan fa’ida da yardar Allah zai samu waraka. Abin sadaqa ayiwa Annabi