Maganin

Hadin Maganin Sanyi ga Maza ga Mata

Assalamu Alaikum jamaa masu Bibiyar wannan shafin

A yau muna tafe da hadin maganin sanyi ga maza da Mata

Ciwon sanyi Yana da illa sosai ga mutane
Yana sa maza da Mata su Zama suna da matsala
Bayan abinda yake haifarwa kamar ciwon kidney, gajiya da Rashin kuzari ta kowace hanya

Hadin maganin

Hadin wannan maganin zai taimaka Maka wajen rage damuwar cutar

A Sami namijin goro guda 3
A Sami citta Mai yatsu Huda 4 KO a Sami dafarnuwa guda 2 sai a jajjaga su
A hada da lemon tsami guda 5

Sai a yanka su kanana kuma a jajjaga su
Shi kuma lemon sai a yanka Shi kanana a matsa ruwan a cikin tukunya kuma a jefa bawon acikin ruwa a tafasa su Duka

Atace kafin a sha idan kuma babu dadin sha to a azuba zuma idan za’asha domin aji dadin Shan nasa
Sai a sha Rabin Kofi sau uku a Rana na tsawon sati 2

In sha Allah za’a Sami nasara

Kada ayi wasa da wannan hadin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button