Maganin
Maganin Ƙarin Ƙiba
wanan magani zai taimaka wajen karin kiba
Abubwan Daza’a Naimu
- Man Hulba
- Zuma
- Sassaƙen kuka
- Chukwi
- Aya
- Ɓawon Kankana
Yanda Za’a Hada Maganin Ƙarin Ƙiba
- Asamu Man Hulba sai a gaurayashi da zuma mai kyau adinga shan chokali biyu mintuna 30 kafin aci abinci. Safe da rana da dare. Za’asha na tsawon sati 3.
- Asamu Sassaƙen babbar bishiyar kuka adaka ashanya yabushe asake dakawa yazama gari sai asamu Aya asoyata sama-sama adaka tazama gari, sai asamu Ɓawon Kankana abusar dashi adaka yazama gari, sai asamu Chukwi adaka yazama gari.
Waɗannan garin sai ahaɗasu guri ɗaya (awunsu yazama daidai) sai a kwaɓa da zuma adinga shan chokali 2 bayan anci abinci. Safe da rana da dare.
Sannan za’a iya gauraya wannan haɗin garin da ruwan Kankana asa madara adinga sha.
Za’asha na tsawon sati uku
